An Bukaci ECOWAS Ta Dauki Mataki Mai Tsauri Akan Gwamnatin Guinea Bissau

9 months ago#HNSTV #HausaNewsSyndicate #HausaSyndicate #HausaNews

Matakin da shugaba Mario Vaz ya dauka don rusa gwamnatin kasar tare da maye gurbinta da wata sabuwa, ya sa kungiyar Cedeao ta gargadi shugaban kasar ta Guinea Bissau ya canza ra’ayi ko kuma ya fuskanci fushinta.

Sai dai da alama wannan barazana ba ta yi tasiri ba,abinda ya sa shugabannin kasashen Afirka ta Yamma kiran wani taro a wannan juma’a a birnin Yamai.

Sai dai,ra’yoyin jama’a sun banbanta dangane da wannan dambarwa domin wasu ‘yan fafitika na ganin kungiyar ta ECOWAS na rufe ido akan wasu batutuwan da ya kamata ta tsawata.

A sanarwar da wani wakilin ECOWAS ya bayar dangane da lamarin, a birnin Bissau, kungiyar ta dibarwa ministocin sabuwar gwamnatin Faustino Imbali wa’adin awoyi 48 su yi murabus ko kuma su fuskanci hukunci.

A ranar 24 ga watan Novamba nan ne ya kamata a gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Guinee Bissau, to amma rashin daidaituwa a tsakanin shugaba Mario Vaz da Firai Minstansa ya sa shugaban rushe gwamnati a watan Oktoba.

A Wannan Tashar Labarai ta Hausa News Syndicate (HNS) muna kukarin gina al’ummar Hausawa a duniya baki daya akan samar da canji.
kawo muku sharhi, rahotannin labarai a cikin Harshen Hausa daga Najeriya, Nijar, Kamaru, Chadi, Benin, Ghana, Sudan, Saudia, Amurka, Ingila da duniya gaba daya.

Muna neman fiye da kanun labarai don fitar da tattaunawa mai ma’ana wacce ke fitar da gaskiyar al’amari . Muna son danganta al’umar Hausawa da ke Yankin Sahara zuwa lamuran da suka fi damun su. Muna bincika gaskiyar bayan hashtags da kuma mutanen da ke bayan ƙididdigar. Za mu nemi gano abubuwan da suke bayan kowane labari.
Ta hanyar sanya ɗan adam a zuciyar kowane labari muna fatan inganta lamiri na duniya wanda ke haifar da kyakkyawar rayuwa – da nuna zurfin fahimta game da bambancin rayuwar da ke kewaye da mu.

#Buhari #ShugabaBuhari #Kwankwaso #RabiuMusaKwankwaso

Zahran Business Centre,
12th floor, Prince Sultan street, A
sSalamah, Jeddah, 21464, Saudi Arabia

#LabaranHausa #BBCHAUSA #VOAHAUSA #Kano #Katsina #Jigawa #Bauchi #Kaduna #Jos #Borno #Maiduguri #Arewa #Hausawa #Fulani #HausaFulani #Nigeria #Niger #Cameroon #Ghana #Niamey #Sudan #Chad #aso #Elrufai #Kwankwasiyya #Atiku #AtikuAbubakar #Adamawa #Zamfara #Sokoto #SarkiSunusi #SarkiKano #AdoBayero #Ganduje #AbdullahiUmarGanduje

source

The Struggle Continues

Leave a Reply

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.